Ahmad Hamisu Gwale
Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da kungiyar yan Kwankwasiyya da za su rika tallata Ayyukan gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf a manhajar Instagram.
Taron kaddamar da kungiyar kungiyar ya gudana karkashin jagorancin kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya wanda yace samar da kungiyar zai tallafi Ayyukan gwamnatin Abba Kabiru Yusuf.
Ibrahim Abdullahi Wayya ya ce an kaddamar kungiyar ne duba da irin tasirin da manhajar Instagram ke da shi a gurin al’umma da kuma taimakawa matasa masu amfani da shafin don samar musu da abin yi.
Tin da fari da take jawabi sabuwar shugabar kungiyar Jamila Auwal Koki ta godewa kwamishinan, sannan ta ba da tabbacin za su yi aiki tukuru domin tallata aiyukan gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Akalla mutum 12 aka kaddamar a domin jagorantar masu tallata Ayyukan gwamnatin Abba Kabiru Yusuf a manhajar Instagram cikin su akwai Jamila Auwal koki shugaba.
Alhajijin kwankwasiyya Gama mataimaki, sai A.A.Ahmad Gwale sakatare, da kuma Jamilu Ahmad Abubakar Ma’ajin kudi.
Sauran sun hadar da, Muhammad Sani Yuba organising secretary, Auwal Muhammad Abubakar sakataren kudi.
Nasir Musa Tofa daraktan yada Labarai, Umar A Anas mai unguwa mai magana da yawun kungiyar, da kuma Aliyu Muhammad Sagagi jamian walwala.
Sauran sune Aliyu Yakubu Sarauta mai magana da yawun kungiyar, da Abbas Muhammad Adam mai daukar hoto, da kuma Aliyu Mukhtar King Haidar a matsayin Content Creator.