Kwamishinan yada Labarai na jihar Kano Ibrahim A. Waiya, ya gudanar da taron Shan Ruwa da yan kungiyar magoya bayan gwamna Abba Kabiru Yusuf da suke yada manufofin gwamnatin a dandalin sada zumunta na Instagram.
Tawagar karkashin jagorancin shugabar kungiyar magoya bayan gwamna a Instagram Jameela Auwalu Koki Mss Meemee, su ne suka shirya taron, a kokarin ci gaba da yada manufofin gwamnatin Abba Kabiru Yusuf a shafin sada zumunta na Instagram.
A jawabinsa kwamishina Abdullahi Waiya ya yabi shugabancin kungiyar magoya bayan gwamna, yana mai kiransu da gwaraza masu yada manufofin gwamnatin Abba Kabiru Yusuf domin tallatawa.
Ya kuma bukaci su sake jajircewa wajen ci gaba da yada manufofin gwamnatin Abba Kabiru Yusuf a shafin na Instagram wanda hakan zai kara fito da irin Ayyukan da gwamnan ke yiwa al’ummar Kano.
Da take nata jawabin tun farko, Hajiya Jamila Auwal Koki shugabar kungiyar, ta nuna jindadin yadda kwamishinan na yada Labarai ke jajircewa da kuma basu goyan goya.
Shi kuwa a nasa jawabin
Daraktan yada labarai na gidan gwamnatin Kano Hon. Sanusi Bature Dawakin Tofa wanda ya samu wakilicin Hon Hassan Tukur Noble Hassan ya bayyana jindadinsa da yadda aka shirya taron shan ruwan.
Taron dai ya samu halartar wasu cikin shugabannin kungiyar magoya bayan gwamna Abba Kabiru Yusuf a shafin sada zumunta na Instagram cikinsu har da A.A. Ahmad Gwale, wanda shi ne sakataren kungiyar.