Rikicin NNPP a Kano : Gwamna Abba ya daina daga wayar Kwankwaso

0

Rahotanni sun bayyana rikicin da ya barke a jam’iyyar NNPP, a Kano, sakamakon yadda Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ki halartar wasu taruka, ya kuma ya ki daga kiran wayar da ubangidansa, Rabiu Kwankwaso.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito Lamarin ya Fara kamari ne tun lokacin da wata kungiyar mai suna “Abba tsaya da kafarka” ta bulla, wadda kuma take kara samun karbuwa a ciki da wajen jam’iyyar NNPP.

Idan za a iya tunawa a ranar 1 ga Nuwamba, wata babbar kotun jihar Abia ta yi hukuncin cewar ta mayar da ikon jam’iyyar NNPP ga tsohon shugaban jam’iyyar, Boniface Aniebonam.

Manya daga cikin wadanda ake ganin Rikicin ya fi kamari akan su sune: sakataren gwamnatin jihar, Baffa Bichi; kwamishinan sufuri na jihar, Mohammed Diggol; kwamishinan ilimi na jihar, Umar Doguwa; Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Kawu Sumaila; da dan majalisar tarayya mai wakiltar Rano/Bunkure/Kibiya.

Wasu yan cikin gida a Kwankwasiyya sun shaida wa Daily Nigerian cewa gwamnan ya riga ya saurari kiraye-kirayen da aka yi masa na cewa ya zama mai cin gashin kansa daga hannun Kwankwaso domin sami damar gudanar da gwamnatinsa da kansa.

Idan za a iya tunawa a ranar Lahadin da ta gabata ne mamba mai wakiltar karamar hukumar Dala a majalisar tarayya Ali Madaki da takwaransa na Rano Kibiya da Bunkure Kabiru Alhassan Rurum suka bayyana ficewarsu daga tafiyar Kwankwasiyya.

Daily Nigerian ta rawaito cewa majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin sun ce a cikin ‘yan majalisar dokokin jihar 26 na jam’iyyar NNPP, wakilai uku ne kawai masu wakiltar Madobi, Nassarawa da Kiru ba sa cikin kungiyar “ Abba Tsaya da Kafarka”.

Kokarin jin ta bakin Kwankwaso ya ci tura, amma wasu majiyoyi na kusa da shi sun zargi gwamnan da jagorantar yiwa ubangidansa na siyasa tawaye tare da daukar nauyin Kungiyar Abba tsaya da kafarka.

Haka zalika shima mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Dawakintofa, ya ki cewa komai kan lamarin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.