Duk wanda ke son barin PDP ya tafi tun yanzu, amma ni ina cikinta zama daram — Bukola Saraki

0

Tsohon shugaban majalisar dattawa ta ƙasa kuma Wazirin masarautar Ilorin Dr. Abubakar Bukola Saraki CON, ya bukaci duk wanda ke shirin fita daga PDP ya fita tun yanzu kafin lokaci ya kure masa.

Saraki ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, wadda mai taimaka masa kan harkokin yada Labarai Abba Gwale ya rabawa manema labarai a Juma’ar nan.

Bukola Saraki na wannan kalaman ne a matsayin mayar da martani bayan wasu jiga-jigan Jam’iyyar ta PDP a jihar Delta sun sanar da ficewarsu a cikin makon nan.

“Bayan ficewar gwamnan jihar Delta daga jam’iyyar PDP zuwa APC, ina ta samun kiran waya daga shugabanni da ƴan jam’iyya matasa da maza da mata, waɗanda suka tsaya tsayin daka wajen ganin an samu ci gaban dimokuraɗiyya.

“Matsaya ta a kan wannan magana shi ne, waɗanda ke son barin PDP su fita tun yanzu, su bar sauran da ke son ci gaba, mu mayar da hankali wajen sake gina jam’iyyar”.

“Yana da muhimmanci duk ɗan Nigeriya ya sani cewa dole ne a tashi tsaye wajen tabbatar da dimokuraɗiyya. Domin tabbatar da hakan, dole ne a samu jam’iyyu masu ƙarfi domin tursasa gwamnati ta yi abin da ya kamata,”.

“Maganar zama jam’iyya ɗaya a ƙasar nan ba abu bane wanda zai zama alheri ba kasancewar ƙasa ce mai addinai daban-daban da ƙabilu daban-daban da yare daban-daban.

Ai abin tsoro ne ma a ce a zauna babu wasu jam’iyyu sai jam’iyya ɗaya, hakan zai nuna cewa mutane ba su da zaɓi, duk abin da aka ga dama shi za a yi musu”

“Saƙona ga ƴan jam’iyya shi ne duk wanda yake son ya tafi ga hanya nan, wanda yake son gyara kuma ya zauna a gyara domin mu samu mutane masu amana, waɗanda za mu dinga rufe ƙofa da su kuma ba za su fitar da maganar a waje ba” a cewar Bukola Saraki.

A ranar Laraba ne Sheriff Oborevwori, gwamnan jihar ta Delta ya bar jam’iyyar PDP ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yayin da tsohon gwamnan jihar Ifeanyi Okowa ke shirin komawa jam’iyya mai mulki nan ba da jimawa ba.

Bukola Saraki ya kuma ce adawa mai ƙarfi na da matukar muhimmanci ga ɗorewar dimokraɗiyya, inda ya ƙara da cewa Najeriya ba za ta iya ci gaba a matsayin ƙasa mai jam’iyya ɗaya ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.