Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure a zauran majalisar kasa, RT Hon. Kabiru Alhassan Rurum ya karbi bakuncin sabbin yansanda 34 da suka fito daga yankin da yake wakilta.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada Labarai Fatihu Yusuf Bichi ya fitar ya ruwaito, Kabiru Alhassan Rurum ya gana da matasan wadanda suka kammala karbar horo, kuma suka zama sabbin Jami’an ‘yansanda ‘yan asalin yankin.
Turakin Rano, ya taya matasan da iyayensu murnar samun wannan dama ta shiga aikin tsaro tare da gargadin su da su kasance jakadun kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure, domin ayi alfahari da su ako ina.
Ya kuma bukaci matasan da su jajirce wajen ci gaba da mayar da hankali kan ayyukansu, har ya bukaci su mayar da hankali domin jin gajiyar abin da suka kowa.
Duka mutanen 34 sun fito ne daga kananan hukumomin na Rano, Bibiya da Bunkure wato RAKIBU.
Kuma wasu cikin wadanda suka yi jawabi kamar Yusuf Shehu Aminu Kibiya da Karibullahi Mansur Rano da Kuma Yusuf Mohd Kulluwa da suka yi jawabi a madadin sauran bayyana godiyarsa ga RT Hon Kabiru Alhassan Rurum, musamman kokarinsa wajen basu kulawa da tallafi a lokacin da suke sansanin daukar horo.