Matasa masu goyon bayan jam’iyyar ADC sun bukaci Kwankwaso Ya Shiga jam’iyyar don Ceto Najeriya

0

Kungiyar ADC Youth Mandate tare da hadin gwiwar ADC Waziran Waziri sun yi kira ga tsohon gwamnan Jihar Kano Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso, da ya shiga hadakar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) domin ceto Najeriya daga halin kunci da tabarbarewar shugabanci da suke zargin gwamnatin APC ta haddasa.

 

Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Babban Mai Kula da kungiyar ADC Youth Mandate, Engr. Ammar Hamisu Dandago, ya sanya wa hannu, inda ya ce Najeriya na fama da matsanancin matsin tattalin arziki, rashin tsaro, rashin aikin yi, da kuma karuwar yanke kauna a zukatan ‘yan kasa.

 

Sanarwar ta zargi gwamnatin APC da kasa samar da hanyoyin magance wadannan matsaloli, tana mai cewa haraji masu yawa, tabarbarewar rayuwa, da rashin daukar mataki mai karfi kan ta’addanci da ‘yan bindiga na kara jefa jama’a cikin wahala.

 

Haka kuma kungiyar ta nuna damuwa kan abin da ta kira yunƙurin mayar da Najeriya kasa mai jam’iyya daya, lamarin da ta ce barazana ce ga tsarin dimokuradiyya.

 

Kungiyar ta bukaci Sanata Kwankwaso da ya hada kai da shugabanni irin su Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amaechi, Nasir El-Rufai, David Mark da Rauf Aregbesola a karkashin jam’iyyar ADC domin samar da sahihin shugabanci.

 

Ta ce kwarewar Kwankwaso, tasirinsa a siyasa, da kusancinsa da talakawa musamman a Arewa, na da matukar muhimmanci wajen karfafa wannan hadaka da dawo da fatan al’umma. Kungiyar ta kuma jaddada kudurinta na ci gaba da wayar da kan matasan Najeriya domin yaki da mummunan shugabanci.

Leave A Reply

Your email address will not be published.