Jam’iyyar NNPP ta bayyana shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, a matsayin wanda ya zama jangwam ga shugaban kasa Bola Tinubu da jam’iyyar mai mulki.
Independent Mirror Hausa ta ruwaito cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu a Juma’ar Nan sakataren yada labarai na jam’iyyar NNPP, Yakubu Shendam, ya ce tsohon gwamnan jihar Kano, ba zai iya ciyo wa Tinubu zaɓe a 2027 ba.
Shendam yana mayar da martani ne ga kalaman da aka ce Ganduje ya furta, inda ya kira Kwankwaso a matsayin wanda ba shi da sa’ar cin zaɓe.
Jam’iyyar ta ce duba da badakalar da ake zargin Gwamna Ganduje ya yi, bai kamata duk wani dan Najeriya mai kishin gaskiya ya dauke shi da muhimmanci ba.
Ya kara da cewa badakalar da ake zargin tsohon gwamnan jihar Kano ya tafka a baya-bayan nan, “lalacewar da ba za ta iya gyaruwa ba, kuma ba zai iya ciyo wa Tinubu da APC zabe a 2027 ba. Tun da Ganduje ya zama shugaban kasa, APC ta riga ta mutu”.
“Ko ana so ko ba a so, Ganduje jangwam ne ga Tinubu, jam’iyyarsa ta APC da kuma ƴan kasa kuma zan iya yin caca da Ganduje a matsayinsa na shugaban kasa, Shugaba Bola Tinubu zai fadi a zaben shugaban kasa a 2027, saboda ƴan Najeriya ba za su zabe shi ba,” in ji Mista Shendam.