Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Kano ta haramta karantawa da sayar da littafin Queen Primer a fadin jihar.
Independent Mirror Hausa ta rawaito shugaban hukumar Abba El-Mustapha ne ya bayyana haka ne ranar Alhamis a yayin da ya jagoranci kwace kwafi-kwafi masu dimbin yawa na littattan.
Littafin yana dauke da wasu kalaman turanci irin su ‘let’s gay’ wato ‘mu shakata’, sai dai wasu na ganin amfani da kalmar ‘gay’ wani sako ne na lalata tarbiyyar jama’a.
El-Mustapha ya ce littafin wanda ke koyar da rubutu da karatu a harshen Ingilishin yana yada “fasadi.”
“Littafin yana cike da maganganu na fasadi wadanda ba su kamata a ce ‘ya’yanmu sun ji su ba kuma an karantar da su ba,” in ji shi kamar yadda ya wallafa a wani bidiyo a shafinsa na Facebook.
Shugaban hukumar ya ce jami’ansa sun kama kwafin littafin guda 1,200 daga kasuwannin da ake sayar da su.