Idan har Abba Gida-Gida ya yi fada da Kwankwaso karshe ko ya jajibo Ganduje ko Shekarau – Ibrahim Musa

0

Guda daga cikin masu amfani da shafikan sada zumunta, Dakta Ibrahim Musa, yace idan har Gwamnan Kano Abba Kabiru Yusuf ya yi fada da Mai gidansa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso to karshe ko ya jajibo Ganduje ko Shekarau domin samun kariya.

Independent mirror ta ruwaito Dakta Ibrahim Musa ya bayyana haka ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Wannan dai na zuwa ne bayan zarge-zarge na fitowa na yadda alamu ke bayyana ana shirin samun sabani tsakanin Gwamna Abba Kabiru da kuma mai gidansa a siyasa Sanata Kwankwaso.

Ibrahim Musa ya wallafa cewa “Idan yan shan kai sukai nasarar hada rikici tsakanin Kwankwaso da Abba, to nima zan koma gefe. Mun taru mun baku goyon baya ne domin a samu hadin kai a kawowa jihar cigaba. Bayan wannan babu abinda muke nema”

“A fahimtata da siyasar Nigeria kowaye kai sai ka samu wani da yake juya ka. Shekarau da aka zuga shi ya bata da Buhari a 2007 sai ya dauko Bashir Tofa ya zame masa godfather. Ganduje da ya bata da Kwankwaso sai ya jajibo Shekarau jikinsa. Idan Abba ya biyewa masu kokarin hada fitina, a karshe dai ko ya jajibo Ganduje ko Shekarau domin samun kariya. A cikin biyu sai anyi daya. Idan ma mutum baiyi sharar masallaci ba zai yi ta kasuwa”

“Ga shi idan rikicin ya barke, gwamnatin zata dare gida biyu ayi ta cin dunduniyar juna. A karshe dai har zabe yazo baza a cimma wani abin kirki ba. Shi yasa muke addua Allah ya hada kan shugabannin mu. Ya kade fitinar da ake son haifarwa ba gaira ba dalili” a cewar Ibrahim Musa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.