Rahotanni sun bayyana kwamitin zartaswa na jam’iyyar NNPP ya kori Sanata Rabi’u Kwankwaso, sakamakon kin bayyana gaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar.
Independent Mirror ta rawaito cewa tin da fari shugabannin jam’iyyar sun dakatar da Kwankwaso, wanda ya yiwa NNPP takarar shugaban kasa a zaben 2023 a babban taron kasa da aka yi a ranar 29 ga watan Agusta a Legas.
A baya dai majalisar zartarwa ta kasa NEC ta NNPP ta kafa kwamitin ladabtarwa ta kuma umurci kwamitin da ya gayyaci Kwankwaso domin ya kare kansa daga zarge-zargen cin hanci da rashawa da kuma karkatar da kudaden jam’iyya/yakin neman zabe cikin kwanaki biyar.
Jam’iyyar ta yi gargadin cewa, rashin bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa zai bayi ga korar Kwankwaso daga jam’iyyar kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada a 2022.
Sakamakon haka, Abdulsalam Abdulrasaq, mukaddashin Sakataren Yada Labarai na NNPP, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Legas, ya ce NNPP ta kori Kwankwaso ba tare da bata lokaci ba saboda ya ki amincewa da gayyatar kwamitin.
Abdulrasaq ya ce: “Majalisar zartarwa ta kasa ta gana a wani zama na gaggawa a ranar Juma’a 1 ga watan Satumba inda ta yanke wannan matakin”
“Bayan kin bayyana da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso yayi a gaban kwamitin ladabtarwa da ya zauna a ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta bayan an gayyace shi a rubuce, an kore shi daga NNPP nan take.
“Za a kai rahoton tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zuwa wuraren da suka dace domin amsa tambayoyi kan karkatar da kudi da yin almubazzaranci da dukiyar al’umma.”
Jaridar Blueprint ta rawaito cewa rikicin cikin jam’iyyar NNPP ya faro ne lokacin da Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar NWC da ke biyayya ga Kwankwaso, ta sanar da dakatar da wanda ya kafa NNPP, Dokta Boniface Aniebonam da sakataren yada labarai na kasa, Dr Agbo Major a ranar 24 ga watan Agusta.