Wasu Ayyukan Gwamna Abba Kabiru Yusuf da ya yi a kwana 100 na mulkinsa

0

A gabatar da gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif ke cika kwana Dari 100 akan karagar mulki, tuni gwamnan ya cimma wasu nasarori a wannan kwanakin.

Independent Mirror ta rawaito cewa Gwamna Abba Kabiru Yusuf wanda aka Rantsar a ranar 29 ga Mayun 2023, ya zama na farko cikin wasu gwanoni da ya cimma wannan nasara.

Cikin wasu manyan Ayyukan da Gwamnan ya gudanar sun hada da sasanta duk wasu basussukan fansho ga wadanda suka yi ritaya daga aikin gwamnatin jihar Kano.

A tsawon kwanakin an soke siyar da Asibitin Yara na Hasiya Bayero tare da gyara shi zuwa Asibiti ga yara.

Dakatar da yankarwa Ma’aikata albashin su, biyan Albashi a duk ranar 25 ga kowane wata.

Tabbatar da samar da ruwan famfo ga gidaje bayan shekaru 8 na rashin ruwa a jihar, budewa tare da gyara manyan makarantu guda 26 da gwamnatin Rabiu Musa Kwankwaso ta kafa kuma gwamnatin Abdullahi Ganduje ta yi watsi da su.

Kula da Kiwon Lafiya da Haihuwa kyauta a asibitin yara na Hasiya Bayero, da biyan Kudin NECO ga Daliban Makarantun Gwamnatin Kano

Amincewa da Biyan kudin Rijistration ga Daliban Kano 7000 a Jami’ar Bayero, da rage kashi 50% na kudin karatu a manyan makarantun jihar Kano.

Haka kuma an dawo da tsarin bayar da tallafin karatu na kasashen waje da na cikin gida na jihar Kano.

Sai kuma amincewa da sake gyara dukkan makarantun firamare da Sakandare na gwamnati baki daya.

Haka zalika an ci gaba da aikin tituna mai tsawon kilomita 5 a wasu daga cikin kananan hukumomi 44.

Da amincewa da fitar da Naira miliyan 72 domin kwasa-kwasai 68 a Kano State Polytechnic da amincewa da kwangilar gina titin Zaria kan naira biliyan 3.6.

Amincewa da gyarawa dalibai gadar tafiya a kafa na BUK, Aminu Kano College of Islamic Studies da Saadatu Rimi University of Education.

Wannan dai kadan ne cikin Ayyukan da Gwamnan Kano Abba Kabiru Yusuf ya gudanar cikin kwanaki Dari 100 a mulkin Kano.

Leave A Reply

Your email address will not be published.