Kotu ta kori karar da Sanusu Kiro ke kalubalantar nasarar Kofa

0

Kotun sauraren kararrakin zabe ta Majalisun tarayya ta Kori karar da Muhammad Sanusi Said Kiru na APC ya shigar gabanta yan kalubalantar nasarar Abdulmumini Jibrin Kofa na jami’iyyar NNPP.

Independent Mirror ta rawaito cewa kutun ta kori karar ne sabida rashin gabatar da gamsassun hujjoji da zasu kalubalaci sahihancin zaben dan majalisar tarayya a kananan hukumomin Kiru/Bebeji, wanda ya baiwa Abdulmumini Jibrin Kofa na NNPP nasara.

Kutun Mai alkalai Uku karkashin jagorancin Mai Shari’a Ngozi Flora ta bayyana cewa takardun da bangarorin biyu suka gabatar a gaban kotun sun nuna cewa Abdulmumini Jibrin Kofa ya ajiye mukaminsa na Babban Sakataren Hukumar Gidajen Tarayya, kwanaki 30 gabanin gudanar da zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu 2023 sabanin da’awar mai kara.

Ta Kuma ce mai shigar da karar ya kasa baiwa Kotun hujjojin cewa an tafka kura-kurai a zaben dan majalisar tarayya na Kiru da Bebeji Inda yace ba’a bin dokar zabe ta 2022 ba a zaben.

“Saboda haka mun kori wannan karar saboda rashin gamsassun hujjoji” a cewar Mai Sharia Ngozi.

Kotu ta kori karar da Sanusu Kiro ke kalubalantar nasarar Kofa

Kotun ta kuma umarci wanda yayi kara da ya biya wanda akai Kara Kuɗi naira Miliyan 100,000.

Leave A Reply

Your email address will not be published.