NLO: Shehu Kilishi ya ajiye aikin da Ramcy FC

0

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Ramcy Gidan Sarki Shehu Kilishi, wanda aka fi sani da Coach Bahago, ya ajiye aikin sa da kungiyar.

Hakan na zuwa ne ta cikin wata sanarwa da wani makusancin sa Nurullahi Babangida ya fitar, kana kuma ya sanya wa hannu.

Babangida yace Shehu ya ajiye Aikin nasa ne ranar 24 ga watan Afrilun nan da muke ciki, bisa wasu dalilai.

Yanzu haka dai kungiyar na tsaka da buga wasanni a matakai daban daban, kamar yadda Babangida ya shaida.

Ramcy kawo yanzu haka na guda cikin kungiyoyin da suke buga gasar NLO da ake fafatawa a wannan shekarar.

Sai dai kawo yanzu babu wani cikakken dalilin ajiye aikin da Shehu Kilishi ya yi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.