Jamilu Uba Adamu
Tun ainahi, matasa su ne ginshiƙin turken jihar Kano. Tarihi ya tabbatar tun tale-tale matasa su ne ginshiƙin cigaban zaman lafiya a jihar, domin matasan wancan zamanin da ya shuɗe su ne jagororin cigaban unguwanninsu tun daga kan aikin gayya, taimakon kai-da-kai da al’amuran wasannin motsa jiki.
A nata ɓangaren, gwamnatin wancan zamanin ta san darajar muhimmancin waɗannan matasan tare da goyon bayansu wajen tabbatar da jawo su a jiki da shigar da su cikin tsare-tsaren al’amuran cigaban matasa a gwamnatance.
Wannan dalili na sanin darajar matasa da gudunmawar da suke bayarwa, musamman wajen gudanar da wasan motsa jiki da tsalle-tsalle, Tsohon Gwamnan jihar Kano, Kwamishinan Ƴan Sanda, Marigayi Audu Baƙo ya ga dacewar gayyatar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na matasa da ke jihar Kano domin gudanar da wasan ƙwallon ƙafa a tsakaninsu a shekarar 1971 domin bikin zagayowar farin cikin murnar samun yancin kai daga hannun Turawan Mulkin Mallaka, wanda ake gudanarwa duk shekara-shekara.
A wancan zamanin, babu wata ƙungiyar ƙwallon ƙafa mallakin gwamnatin jiha kamar yadda ake da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars wacce aka ƙirƙira a shekarar 1990, don gwamnatin mulkin soja ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Ƴansanda, Marigayi Audu Baƙo ta nemi ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na unguwanni irin su Zumunta Fagge, Young Boys Club (YBC) Fagge.
Sauran sune Ƙofar Wambai, Tudun Wada Patriots FC, Darma United, Black Scorpion, ECN, da sauransu da su zaɓo ƴan wasan ƙwallon ƙafa daga ƙungiyoyinsu don gudanar da wannan wasa da za a gudanar don su wakilci da a ranar wasan za ta ɗauki sunan Gwamna da sunan Sarkin Kano (Governors team and Emir’s team).
Bayan sanarwar buƙatar gwamnati a kan haɗa wannan gagarumin wasa ta samu waɗannan matasa waɗanda suka haɗa da Mallam Mukhtar Atamma, Hamza Usman Darma, Nasidi AC Fagge, Ibrahim Abba Fagge, Ustaz Najume, Ammani Inuwa Fagge, Uba Badariya, Alh. Sikiru,da Babangida Bello wanda a zamanin su ne jagororin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da aka gayyata don wannan wasa. 
Daga nan suka taru a unguwar Fagge a masallacin Mallam Atamma suka yanke hukuncin bijirewa wannan gayyatar da gwamnati tai musu bisa nuna rashin jin daɗin yadda gwamnati ba ta taimakon ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar da suke jagoranta.
Kuma suka zartar da cewar tabbas ba za su bari magoya bayan ƙungiyoyin nasu su halarci wannan wasan ba.
Kamar yadda ɗaya daga cikin waɗancan matasan da aka yi wannan lamarin da su ya taɓa faɗa min cewar bayan gwamnati ta samu rahoton ƙin amincewarsu a kan gudanar da wannan wasan, sai jami’an gwamnati suka nuna wa Gwamna Audu Baƙo cewa matasan nan kurari kawai suke yi ba su da wani nauyi ko tasiri wajen cika filin wasa.
Hakan ne ya sa aka haɗa wasa a tsakanin Rundunar Ƴansanda da ta Sojoji domin su gudanar da wasan a madadin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar matasan nan.
Gwamna Audu Baƙo yai murna da wannan shawara ya kuma ba da izinin ai wannan wasa kamar yadda aka ba shi shawara.
Bayan duk an gama shirye-shirye da sanarwar a kan wannan gagarumin wasan, Gwamna, Sarkin Kano da jami’an gwamnati sun zuwa filin wasa, amma kash! banda jami’an tsaro da jami’an gwamnati ba matasa ko yan kallo duk da kuwa da sanarwar da akai ta yi. 
Dalilin kuwa shi ne matasan unguwar Fagge, Cikin Birni da Tudun Wada duk sun haɗa kai wajen kauracewa wannan wasa da gwamnati ta haɗa.
A wannan ranar da akai wasan an ce ran Gwamnan Kano, Marigayi Audu Baƙo ya ɓaci matuƙa kasancewar rashin ganin matasa da ƴan kallo a filin wasa duk da tabbacin da jami’in gwamnati suka ba shi.
Yana komawa gidan gwamnatin Kano ya na tuɓe farar safar da ke hannunsa cikin fushi da jami’in gwamnatin da suka ba shi shawara kafin wasan yake furta cewar: ” Ashe Matasan nan su ne Pillars ɗin Kano ba ku ba.”