Kungiyar Masu Horarwa reshen Kano Sun Ziyarci SWAN Kan rikicinsu da Audu Maikaba

0

Kungiyar Masu horar da yan wasan Kwallon Kafa sun ziyarci kungiyar marubuta labaran wasanni ta kasa reshen Kano SWAN bayan rikicin da ya faru da su da mai horar da Kano Pillars Abdullahi Maikaba.

Kungiyar karkashin jagoranci Mai Shari’a Ibrahim Gwadabe ta kai ziyarar sansantawa ne kan rikici daya barke tsakanin bangarorin biyu a yunkurin magance Matsalar.

Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun kungiyar ta NFCA Jabir Hassan ya fitar tace sun Tattaunawa manyan batutuwa da kawo yanzu haka rikicin na gabda zuwa karshe.

Maishari’a Gwadabe wanda ya dau dogon lokaci yana bayani kan rawar da kungiyar marubuta labarin wasanni ke takawa wajen cigaban masu horar da yan wasan kwallon kafa da yan wasa a kyano, yayi mamakin yadda cikin kankanin lokaci aka samu sabanin da zai iya rusa cigaban da a wannan lokaci ake ganin jihar kyano ta samu a wannan fanni.

Inda ya bukaci bangarorin biyu dasu maida takobi cikin kube, tare da alkawarin duk mai yiwuwa dan kawo karshen wannan dambarwa da kawo yanzu haka ke ci gaba da daukar hankali.

Anasa jawabin maitamakin shugaban kungiyar marubuta labarin wasanni ta kasa reshen Kano Abubakar Sadiq ya yabawa kungiyar masu horar da wasan kwallon kafar ta kano bisa yadda suka nuna damuwarsu da abin dake faruwa.

Ya kuma yi alkawarin basu dukkan hadin kan da suke nema dan kawo cigaban wasan kwallon kafa a jihar Kano dama kasa baki daya.

Rahotanni sun bayyana a karshen makon daya gabata ne aka samu wata rashin fahimta tsakanin kungiyar SWAN da zargin Audu Maikaba da kalaman cin zarafi ga daya daga cikin ya’yan kungiyar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.