Gidauniyar ADG Care Foundation ta Horas da mata 6500

0

Gidauniyar ADG Care Foundation ta gudanar da gagarumin taron horas da mata 6,500 a yankin Kano ta Arewa domin karfafa musu guywa tare da koya musu kananun sana’o’i domin su dogara da kan su. 

Jaridar Independent mirror ta ruwaito cewa an gudanar da Horas war a garin Garo dake Karamar hukumar Kabo ta jihar Kano inda mata daga sassa daban-daban suka halarci wannan guri domin koyon sana’o’in hannu da kuma samun tallafi don fara sana’o’in su.

Gidauniyar ADG care foundation hadin gwiwa da Fhuzee, Beyond the Barrier Initiative ne suka gabatar da shirin a wani bangare na inganta rayuwar ‘ya ‘ya mata a wannan yanki.

Shugaban gidauniyar ADG care foundation Engr. Rabi’u aliyu Garo, ya bayyana cewa sun himmatu wajen ganin sun samar da duk wani hora na dabarun koyawa mata sana’oin dogaro da kai domin suma su bunkasa sana’o’in su wanda hakan zai taimaka wajen Inganta rayuwar su.

A wata sanarwa da Daraktan sadarwa da hurda da jama’a na gidauniyar Ya fitar Aliyu Abdul Garo, Ya bayyana cewa gidauniyar a shirye take wajen cigaba da tallafawa harkokin Ilimi, lafiya, Matasa da sauran Al’amuran yau da kullum.

Leave A Reply

Your email address will not be published.