An Karrama Hon. Makki Yalleman sakamakon samawa matasa fiye da 100 aikin dan sanda

0

Al’ummar karamar hukumar Malam Madori da Kaugama dake jihar Jigawa sun karrama dan majalisa mai wakiltar su, Hon. Makki Abubakar Yalleman bisa kokarin da yake yi wajen samar da cigaba da ayyukan yi ga matasan yankin.

Karramawar ta zo bayan matasa sama da 100 sun samu gurbin aikin dan sanda daga kananan hukumonin biyu, wanda duka suka samu ta hannun dan Majalisar.

Hon. Makki Abubakar Yalleman wanda shine shugaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin yan sanda yayin karbar karramawar, yayi kira ga matasan da su gudanar da ayyukan su cikin kwarewa tare da jajircewa.

An karrama dan Majalisar a wata liyafa da iyalan yan sandan suka shirya, sun bayyana godiyar su gareshi tare da yi masa adduo’i da fatan alkairi.

Matasan guda 137 sun fito ne daga mazabar sa da wasu bangarori na arewacin Najeriya.

Dallatun Hadeja, Alhaji Usman Ginsau wanda ya wakilci Mai Martaba Sarkin Hadeja ya yaba wa Dan Majalisar bisa ayyukan cigaban da yake kawo wa yankin.

Hakazalika, shugaban Jam’iyyar APC na yankin Hadejia, Alhaji Abdullahi Ango ya bayyana wannan yunkuri a matsayin wata nasara da jajircewa da kwazon dan Majalisar.

Hon. Makki ya kuma jaddada cigaba da bada goyon bayan sa ga cigaban yankin da ma jihar Jigawa baki daya don bunkasa Jihar da samar da cigaba mai dorewa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.