Gwamnatin jihar Katsina ta sanar Da rushe shugabancin gudanarwar Kungiyar nan take.
Independent Mirror ta rawaito kwamishinan matasa da wasanni, na jihar, Hon. Yusuf Rabi’u Jardede ya bayyana rusa shugabancin ƙungiyar a wata sanarwa da ya fitar mai kwanan watan 11 ga Oktoban Da muke ciki na Shekarar 2023.
A cikin takardar ya kuma bayyana nada kwamitin mai dauke da mutane hudu da zasu tafiyar da harkokin ƙungiyar kafin a naɗa sabbin shugabanni.
Hon. Yusuf Jardede ya bayyana cewa matakin na ɗaya daga cikin ƙoƙarin da Gwamnatin jihar keyi na inganta harkar wasan ƙwallon ƙafan a jihar Katsina.
Cikin sabbin mutum hudun da zasu jagoranci Katsina United sun hada Da…
1-Alhaji Kabiru Danlami Rimi (KADMASH)
2- Gaddafi Muhammad Rudwan
3-Aminu Abdullahi Leno.
4-Abubakar Sani.
Tuni ma dai Sanarwar ta umarci tsaffin shugabanni masu tafiya da su mika ragamar shugabancin kungiyar ga kwamitin nan take.
Haka zalika sanar ta kuma ya bawa tsaffin shugabanni da suka jagoranci Katsina United, tare da yi musu fatan Alkhairi.