Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya yi watsi da zargin da Sanata Elisha Abbo ya yi cewa yana da hannu a ƙwace nasararsa da kotun ɗaukaka ƙara ta yi a ranar Litinin.
Jaridar Independent Mirror ta rawaito cewa da yake magana da manema labarai, mai magana da yawun shugaban majalisar ta dattawa, Eseme Eyiboh, ya ce ba shi da hannu a hukuncin da kotun ta yanke.
Eyiboh ya ce “Abin takaici ne idan Abbo ya yi zargin cewa da hannun Akpabio a ƙwace nasararsa. Yana neman wanda zai ɗora wa lafi ne kawai.
“Kotun Ɗaukaka Ƙara a ƙasar nan na yanke hukunci ne bisa tanadin dokar zaɓe da kuma irin hujjojin da masu ƙara suka gabatar. Shugaban majalisar dattawa ba shi da wani dalili na yi wa wani ɗan majalisa bita-da-kulli.”

Tun da farko dai, bayan ƙwace nasararsa da kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta yi, Sanata Abbo ya yi zargin cewa Godswill Akpabio na da hannu a lamarin.
Hukuncin na nufin Mista Abbo ya bar Majalisar Dattawan Najeriya ke nan kasancewar ita ce kotun ƙarshe da ke da hurumin sauraron ƙorafin zaɓen ‘yan majalisa – ma’ana babu sauraron ɗaukaka ƙara.
BBC