Gwamna Abba Kabir ya raba kayan wasanni ga kungiyoyin kwallon kafa 600 na Kananan hukumomin Kano

0

Ahmad Hamisu Gwale 

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya raba kayan wasanni ga kungiyoyin kwallon kafa 600 da suke a fadin Kananan hukumomin jihar.

Gwmna Abba Kabiru ya jagoranci raba kayan wasannin ne a ranar Alhamis 28 ga Nuwambar 2024 a dakin taro na Coronation da ke gidan gwamnatin jihar.

A jawabinsa yayin bayar da tallafin kayan wasannin, Abba Kabir Yusuf, ya ce suna kokarin farfado da wasan kwallon kafa da sauran wasanni, har ma da yin abubuwa da zasu karfafawa Kano Pillars gwiwa.

Ya kuma yi alkawarin gyara filayen wasanni na kananan hukumomin Kano 44 wanda hakan zai sa matasa su ci gaba da yin wasanni daban daban.

Da yake nasa jawabin kwamishinan matasa da wasanni na Kano Mustapha Rabi’u Musa Kwankwaso, ya godewa gwamnan Abba Kabir Yusuf bisa gudunmawar da yake baiwa harkokin wasanni.

Ya kuma bukaci wadanda aka bawa tallafin kayan wasannin su tabbatar sun yi amfani da su domin habbaka wasanninsu.

Cikin kayan wasannin da Gwamna Abba Kabir ya rabawa kungiyoyin kwallon kafar sun hadar da rigunan sawa, da safuna da kuma Kwallo ta bugawa.

Taron dai ya samu halartar kwamishinonin Gwamnatin Kano, da tsaffin shugabannin hukumar wasanni da masu ci, har mada shugancin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.

Leave A Reply

Your email address will not be published.