Ana zaman dar-dar bayan Yan bindiga sun harbe wani dan wasa a kasar Panama

0

Rahotanni sun bayyana an harbe Gilberto Hernández ɗan wasan kwallon kafa na ƙasar Panama a birnin Colón.

Independent Mirror ta rawaito cewa yan bindigar sun buɗe wuta kan rukunin wasu mutane, ciki har da Gilberto Hernández, mai shekara 26, wanda ke jikin wani gini a birnin.

Hernández ya rasu sannan ƙarin mutum takwas sun jikkata a harin.

Sai dai, babu tabbacin cewa ɗan wasan, wanda ke buga wa kungiyar Atlético Independiente, shi aka yi niyyar kai wa harin.

Ana samun ƙaruwar mutane da ake kashewa a Colón a cikin watanni da suka gabata, yayin da wasu gungun ƙungiyoyi biyu ke faɗa da juna don samun iko da wuraren da ake bi wajen safarar miyagun ƙwayoyi.

Zuwa yanzu, sama da mutum 50 aka kashe a Colón, birnin da ke da mutum 40,000 a cikin shekarar nan.

Birnin da ke arewacin Panama, ya kasance hanyar da ake bi wajen safarar hodar-iblis daga Kudancin Amurka zuwa Panama sannan a zarce zuwa Turai.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Wasu ƴan bindiga guda biyu sun tursasa wa wani direban taksi da ya kai su wani wuri mai maƙwabtaka da birnin Barrio Norte, inda bayan isar su kawai suka fara buɗe wa mutanen da suka taru wuta.

Gilberto Hernández
                Gilberto Hernández

Gilberto Hernández ya fara buga wa ƙungiyar kwallon kafar Panama wasa a watan Maris ɗin bana, a wasan da suka fafata da Guatemala.

Mahaifin ɗan wasan ya buƙaci shugaban matasan Colón “ya dakatar da wannan tashin hankalin”, inda ya yi kira ga hukumomi, su ƙaddamar da bincike don gano masu laifi.

Ƙungiyar ƙwallon kafar Panama da kungiyar Gilberto Hernández, sun miƙa ta’aziyyarsu ga iyalansa kamar yadda BBC ta wallafa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.