Kotun sauraron kararrakin zaɓen shugaban ƙasa za ta yanke yanke hukunci kan karar da aka shigar gabanta a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba.
Independent Mirror ta rawaito magatakar na kotun ɗaukaka ƙara, Umar Bangari, shi ya bayyanawa manema labarai hakan yau Litinin, inda ya ce za a kuma yaɗa zaman kotun kai-tsaye.
Ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da takwaransa na Jam’iyyar Labour Peter Obi da kuma na jam’iyyar APM, sun shigar da ƙara a gaban kotu inda suke kalubalantar sakamakon zaɓen da ya bai wa Shugaba Bola Tinubu nasara a zaɓen da aka gudanar ranar 25 ga watan Febrairu.
Ƴan takarar jam’iyyun sun kuma buƙaci kotu ta soke zaɓen saboda zargin tafka maguɗi da suka an yi kamar yadda BBC ta wallafa.