Ahmad Hamisu Gwale
Mai horar da tawagar Super Eagles B Augustine Eguavoen, ya saka sunan Aminu Sani Adam na Kano Pillars cikin ‘yan wasan kwallon kafa na Najeriya 30 da ya gayyata.
Cikin ‘yan wasan da aka bayyana, zasu isa Sansanin tawagar Super Eagles da ke Ikenne na jihar Ogun domin shirin buga wasa da kasar Ghana a wasan farko na shiga gasar cin kofin nahiyar afrika ta yan wasan cikin gida.
Sauran da aka kira daga Pillars sun hada da Abiam Nelson da kuma Rabi’u Ali wanda ya ci kwallo 8 a wasannin Premier ta kasa NFPL.
Aminu Adams Sani ya bugawa Kano Pillars wasa 14 kakar bana, wanda ke zama cikin yan wasan da zasu fafata a tawagar ta Super Eagles ta yan wasan gida.
Ana saran wasan farko da Super Mario B za suyi da tawagar Ghana zai gudana a filin wasa na Accra Sports Stadium a ranar 22 ga Disambar da muke ciki.
Sai kuma wasa na biyu da zai gudana a filin wasa na Godswill Akpabio da ke birnin Uyo a ranar Asabar 28 ga Disambar shekara da muke ciki.
Jumullar yan wasa 30 da aka gayyata domin isa sansanin tawagar Super Eagles B sun hada da masu tsaran raga Henry Ozoemena (Enyimba FC); Kayode Bankole (Remo Stars); Nurudeen Badmus (Kwara United)
Yan wasan baya kuwa Ismail Sadiq (Remo Stars); Waliu Ojewole (Ikorodu City); Imo Obot (Enyimba FC); Taiwo Abdulrafiu (Rivers United); Junior Nduka (Remo Stars); Victor Collins (Nasarawa United); Ifeanyi Onyebuchi (Rangers International); Steven Mayo (Rivers United)
Yan wasan tsakiya sun hada da Jide Fatokun (Remo Stars); Rabiu Ali (Kano Pillars); Saviour Isaac (Rangers International); Musa Zayyad (El-Kanemi Warriors); Emmanuel Ogbole (Kwara United); Papa Daniel Mustapha (Niger Tornadoes); Kazeem Ogunleye (Rangers International)
Yan wasan gaba kuwa akwai Anas Yusuf (Nasarawa United); Adamu Abubakar (Plateau United); Osy Martins (Lobi Stars); Sikiru Alimi (Remo Stars); Temitope Vincent (Plateau United)
Sauran sune Samuel Ogunleye (3SC); Abiam Nelson (Kano Pillars); Meyiwa Oritseweyimi (Bendel Insurance); Ngbemena Ikechukwu (Heartland FC); Sunday Megwo (Abia Warriors); Umar Al-Amin Ibrahim (El-Kanemi Warriors); Adams Aminu Sani (Kano Pillars)