Fafutukar Kare Hakki: Tunkarar Matsalar Cin Zarafin Mata da Kananan Yara a Maiduguri

0

Daga Amina Abbagana

Ina zaune kan kujera ta a wani karamin dakin labarai dake birnin Maiduguri, ina kallon yanda wata iska ke kadawa daga waje, a birnin da dimbin jama’a ke rayuwa. 

Sai dai duk da haka zuciya ta kamar ta fashe saboda irin mummunan labarin da idona ya gane min.

Labari ne mai matukar sosa rai da tayarda hankali.

Labari ne da aka kasa kawar da shi a cikin al’umma duk kuwa da irin rubuce-rubucen da na yi akansa.

Batun Cin zarafin mata da kananan yara a Najeriya matsala ce da ke ci gaba da ci wa masu ruwa da tsaki a ƙasar tuwo a ƙwarya.

Hanyoyin cin zarafin sun haɗa da lakaɗa musu duka da yi musu fyaɗe da wasu abubuwa da dama.

Ko a nan birnin Maiduguri, fadar gwamnatin jihar Borno wanda tashe-tashen hankula ya dai-daita a shekarun baya, akwai irin wannan matsala.

Na sha yin rubutu akan wannan matsala ta cin zarafin mata da kananan yara, wani lokacin na kan yi mamaki harma na tambayi kai na: shin anya kuwa ina yin abinda ya dace? wai zan nade kafufuwana a cigaba da cin zarafin mata da kananan yaran kuwa?

Na tuna wata yarinya mai suna Aisha ‘yar shekara 16 wadda a baya ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da ita. Labarin ta ya kasa gushewa daga kwakwalwata.

Muna zaune da ita a wata cibiyar gyaran hali, da ka kalli kwayar idanunta, ba bu shakka kasan akwai damuwa tattare da ita saboda tsabagen ukubar da ta fuskanta.

Ni kai na ban san lokacin da na zubar da kwalla ba sakamakon halin kuncin da na iske ta a ciki.

“Aisha ta shaidamin cewa kokadan ba ta yi tsammanin za ta dawo a raye ba,” Ta na magana kasa-kasa, muryar ta da alama ba bu sauran karsashi kamar ganyen bishiyar da ya bushe ya fado kasa. ” Ta ce lokacin da na kubuta daga hannun ‘yan’tadda na dawo gida, na fuskanci babban kalubale saboda jama’ar da ke nan kwata-kwata basu dau ke ni a matsayin Aisha ba. Su kan kira ni ‘matarsu’.’ Ba zan ta ba mantawa ba.”

Kai, intakai ce muku rayuwar Aisha za ta iya karewa a can, sakamakon kyama dakuma abin kunya.

Sai dai kamar yadda masu iya magana ke cewa ‘Zakaran da ALLAH ya nufa da cara ko ana muzuru ana shawo sai ya yi’, da taimakon kungiyoyin sa-kai na cikin gida hadin gwiwa da ma’aikatar mata, Aisha ta sami horo kan sana’o’in dogaro da kai.

Yanzu haka, Aisha na gudanar da sana’ar dinki wadda ta ke samun dan taro da sisi domin ta tsira da mutumcin ta.

Ama har yanzu, juriya da jajircewar da ta yi, bai gamsar da ni ba. Bana iya cire mata tsananin ukubar da ta shigaba a baya, na dai yi Labarin ta ne kawai bisa abinda idanuna suka gane min.

Gwamman shekaru, hukumoni da shugabannin addinai da kungiyoyin sa-kai na bullo da shirye-shirye danufin kawo karshen cin zarafin mata da kananan yara a kasar nan.

Guda daga cikin irin wadannan shirye-shirye shi ne wani kudiri na yaki da cin zarafin mutane wato Violence Against Persons Prohibition Act (VAPP) a turance, wanda galibin Jihohin Najeriya suka amince da shi.

Kudirin ya yi tanadi domin shawo dukkan wani nau’i na cin zarafin mutane a cikin gida, kama daga cin zarafi ta hanyar lalata dakuma na tursasawa. Ga misali a Jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, sarakunan gargajiya na ba da gudunmawa matuka wajen kawo karshen wannan matsala, ta hanyar amfani da baiwa da shikima gamida kwarjinin da su ke da shi wajen jan hankali al’umma game da abinda ya shafi yin kaffa-kaffa da batun al-ada dakuma dabi’a.

Na halarci wata ganawa da aka yi a garin Konduga, inda limamin garin ya yi jawabi gaban al’umma. “ Ya ce haramun ne a cutar da ‘Ya mace ko ta wacca siga,” ya cigaba da nuna illar dake tattare da cin zarafin mata da kananan yara, kuma bisa dukkan alamu jama’ar da ke wurin sun fadaka.

Jawabin da Limamin ya yi, na zuwa ne watanni bayan horo da kungiyoyin sa-kai suka shirya, wanda ke kokarin shigo da malaman addini kasancewar su masu ruwa da tsaki wajen yaki da nuna ban-bancin jinsi.

Wannan yunkuri bai tsaya iya nan ba, tun bayan samar da wani sashen yaki da cin zarafin Al-umma da aka yi a Caji-ofis din ‘yan sanda a birnin Maiduguri, mata da dama na cigaba da kai koke gameda cin zarafin su da aka yi.

Wata Jami’ar ‘yan sanda dake caji-ofis din Gwange ta shaidamin cewa sukan karbi korafe-korafe na cin zarafi sosai, amma a fili ta ke, fadakarwar da ake yi na yin tasiri wajen karfafa gwiwar matan da aka ci zarafinsu, su fito su magantu.

“Shekaru goma baya jama’a kan yi shiru idan aka ci zarafinsu,” acewar jami’ar ‘yan sandan. “Amma yanzu mata sun farka daga dogon baccin da suka yi a baya.”

Sai dai duk da haka, a iya cewa wannan nasara, ta yi kadan la’akari da girman matsalar. Magana ta gaskiya, Cigaban da ake samu ya dore, amma hakika akwai jan aiki a gaba.

A wata ziyara da na kai sansanin ‘yan gudun shijira dake Dalori, na yi arba da wata baiwar ALLAH Halima, bazawara mai yara uku. An kashe mijinta lokacin ayyukan ta’addanci, lamarin da ya barta da marayu cikin tagayyara.

Ta kan ji takaici tareda rusa kuka duk lokacin da ta zo kwanciya da daddare, ba komai ba ne ya ke ma ta ciwo, face makomar ‘ya’yan ta mata guda uku.

Ta sami dauki daga hadakar kungiyoyin mata wanda majalisar dinkin duniya ke tallafawa, kuma tallafin ne ma ya sauya rayuwar ta. Sun ba ta horo kan sana’ar dogaro da-kai tareda bata jari domin cigaba da gudanar da sana’ar hada sabulu.

Babbar D’yar Halima wato, Amina, ta na zuwa makaranta karkashin wani tallafin karatu da wata kungiyar sa-kai ta ba ta.

Farin ciki da godiyar Halima ba zai misaltu ba, amma ta na fargaba idan taimakon da ta ke samu ya yanke. “me zai faru? Idan har gamayyar kungiyoyin da ke tallafa ma ta suka janye? Mu marasa galihu ne har yanzu” acewar Halima.

Wannan fargaba da tambaya ta sa ni tuntuntuni matuka. Ta ya ya zamu tabbatar wannan tallafi da ta ke samu ya dore? Ta ya ya za mu kare sauran mata kamar Halima idan lamura sun sauya?

A matsayi na, na kwararriya kuma gogaggiyar ‘yar jarida, da na shaida halin da mutanen da aka ci zarafin su ke ciki, sa’annan har yanzu, na kasa tabuka wani abun kirki na yi gum da baki na. Mu kan rubuta kanun Labarai da yin rahotonni ba tareda wani abu ya biyo baya ba. Kuma mata da kananan yara da ake cin zarafin su, ba sa gani a kasa.

A wasu lokutan, na kan iya tuna hirarraki da amsar da na ke samu daga wurin mutane.

Labarin mata kamar Aisha da Halima kan zo mini a zuciya, kuma na kan ji shakku ko rahonnin da na ke yi kan cin zarafin mata da kananan yara zai kawo sauyi gameda wannan matsala.

Amma duk da haka yin shiru ba shi ne mafita ba. Idan har ba mu fadawa duniya irin wadannan labarai ba, to su waye ya kamata su fada? Muddun ba mu kara kaimi wajen tabbatar da yin abinda ya dace ba, to waye zai saurare mu har ya share mana hawaye?

Tabbas kawo karshen cin zarafin mata da kananan yara abu ne dake bukatar karin fadakarwa; da kuma sauya tsarin rayurmu. Ilimi shi ne ginshikin komai na rayuwa musamman wajen koyar da kananan yara muhimmancin sanin ya kamata, dakuma nunawa ‘ya’ya mata kima da darajar da su ke da ita a cikin al’umma.

Zalika gwamnati bai kamata ta tsaya iya bijiro da dokoki kawai ba, ta tabbatar an aiwatar da su yanda ya da ce. Su kuma wadanda ake samu da aikata wannan laifi a tabbatar doka ta yi aiki akan su, ba sani ba sabo. Harwayau kungiyoyin sa-kai ka da su yi kasa a gwiwa wajen tallafawa wadanda aka ci zarafinsu ta hanyar basu shawarwari da kuma koya musu sana’o’in dogaro dakai.

Haka kuma masu rike da sarautun gargajiya da shugabannin addinai dana al’umma wajibi su kara himma, su kuma kafafen yada labarai alhakin su ne su cigaba da wayar da kan jama’a illar cin zarafin mata da kananan yara ta hanyar gudanar da binciken kwa-kwaf.

Sai dai duk da wadannan matakai, nima sai na kara kaimi.

Ya yinda na ke kammala wannan rubutu, zuciya ta cike ta ke da rashin nutsuwa, sakamakon halin da ‘yan uwana Aisha da Halima suka shiga, hakika labarinsu ya tsumani ya kuma sauya tunani.

Ni ba ‘yar jarida ba ce kadai; ni mace ce, ‘Dyah, kuma ‘yar uwa. Don haka abinda ya shafe su, ya shafe ni nima, kamar abin nan da masu iya magana ke cewa ‘Ciwon ‘Dyah mace na ‘ya mace ne.

Bugu da kari wannan labari ba na su ba ne su ka dai, na mu ne ba ki daya. A saboda haka muddun aka cigaba da cin zarafin mata da kananan yara, to kuwa shakka babu zan cigaba da yin rubutu akai. Zan cigaba da daga murya, ba zan gajiya ba, har sai mata da kananan yara a Maiduguri da sassan Najeriya suna gudanar da rayuwarsu ba tare da tsoro ko shakkar abinda ka je ka dawo ba.

Bisa la’akari da cewa sun cancanci su yi rayuwa mai inganci cikin nishadi da walwala. Sun cancanci a martaba su, sun kuma cancanci zaman lafiya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.