Bikin Bude Filin Wasa na Dambatta: Barau FC da Kano Pillars sun tashi 1-1

0

Kungiyar Kwallon kafa ta Barau FC tayi 1-1 da abokiyar burminta Kano Pillars a wani wasan sada zumunta da suka fafata a ranar Juma’a 29 ga Nuwambar 2024 a garin Dambatta.

Wasan da ya gudana tsakanin Barau FC da Kano Pillars, an shirya ne domin bikin bude sabon filin wasan Dambatta mallakin kungiyar ta Barau FC.

Dan wasan Kano Pillars Akpesiri Naibe ne ya fara zura kwallon farko a minti na 3 da fara wasan, sai Mujahid Abubakar ya warwarewa Barau FC a minti na 5.

Sai dai a minti na 30 dan wasan Barau FC Chijioke Williams ya barar da bugun daga kai sai mai tsaran raga, wanda golan Kano Pillars ya ture a yayin wasa.

Barau FC wadda ke shirye-shiryen gasar NNL ta bana, ta buga wasan ne domin kara karfin kungiyar da a yanzu hankula suka karkata a kanta.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibrin, shi ne wanda ya gina filin wasan da kungiyar ta Barau FC zata rika buga wasannin gida a gasar ta NNL.

Dubban magoya baya ne suka halarci kallon wasan da aka gudanar a ranar Juma’a a garin Dambatta da ke arewacin jihar Kano.

Barau FC za ta karbi bakuncin Mighty Jet’s FC
a wasan farko na gasar Firimiyar Najeriya mai daraja ta biyu ta NNL ta kakar 2024/2025 a wasan da zai gudana a ranar 7 ga Disamba mai kamawa.

Ana saran filin wasa na Dambatta da ke arewacin jihar Kano, shi ne zai karbi bakuncin wasan farko da Barau FC da Mighty Jet’s FC za su kece raini da junansu.

A ranar 30 ga Nuwambar da muke ciki ne za a fara wasan farko a gasar ta NNL a wasan da Abaliki FC za ta kece raini da Madiba FC a filin wasa na Ngele Oruta da ke jihar Ebonyi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.