Mai tsaran raga na kungiyar Kwallon kafa ta Turbo Touch International Saleem Musa Dogo na ci gaba da haskawa a kakar wasanni ta wannan shekarar.
Saleem Dogo dan asalin unguwar Birged din karamar hukumar Nassarawa a nan jihar Kano, kawo yanzu haka tauraruwarsa na ci gaba da haskawa a kungiyar sa.
Dogo wanda aka haifeshi a Ranar biyu ga watan Satumbar shekarar 2007 yana bugawa Kungiyar Turbo Touch wasa a matsayin mai tsaran raga.
Ya bugawa Turbo Touch International wasa 57, inda ya hana kwallo 15 shiga raga, sannan ya taimaka aka ci Kwallo 7 a matsayinsa na mai tsaran raga.
Ga yadda Saleem Musa Dogo ya taka rawar gani a wasannin da ya bugawa Kungiyar Turbo Touch International dake nan jihar Kano.
Ya buga wasa 57.
Ya hana kwallo 15 shiga raga.
Ya ture bugun daga kai sai mai tsaran raga 12.
Ya Taimaka an ci kwallo 7.
Da kansa ya ci kwallo 3.