SADIYA ICAN KABARI, TA GURFANA A GABAN KOTU BISA TUHUMAR TA DA BATA SUNA.

0

SADIYA ICAN KABARI, TA GURFANA A GABAN KOTU BISA TUHUMAR TA DA BATA SUNA.

Daga Ibrahim Aminu Riminkebe.

Matashiyar ‘yar siyasa Sadiya Dauda Ican kabari ta gurfana yau a gaban babbar kotun shari’ar musulinci dake zaman ta a unguwar Shahuci a nan kano, karkashin jagorancin mai shari’a Malam Abdu Abdullahi Waiya, a bisa zargin ta da bata sunan mahaifin dan siyarar nan Adamu Abdullahi Karkasara.

A baya dai kotun ta bada umarnin like wa wacce ake zargin sammacin a kofar gidan ta da aike mata da sakon ta takwana da kuma hanyar kafar zamani wato WhatsApp, biyo bayan yadda ake zargin ita Sadiya Dauda Ican kabari tana gujewa shari’a.

A zaman kotun na yau laraba wacce zargin Sadiya Ican kabari ta bayyana a gaban kotun bayan Karbar sammacin da kotun ta bada umarnin a like mata a kofar gidan nata.

Lauyan mai kara Barista Tanimu Yahaya, ya bayyana kotun cewa, wacce tuhumar Sadiya Dauda Ican kabari tayi wani bidiyon inda ta bata sunan mahaifin mai kara ta Kuma yada bidiyon a kafafan sada zumunta.

Barista Tanimu Yahaya ya sake shedawa kotun cewa, kalaman da ita Sadiya Ican kabari tayi amfani dasu sun tayar da hankulan dangin mai kara, a inda yace yau shekaru asirin da biyar da rasuwar mahaifin Adamu Abdullahi Karkasara.

Lauyan mai karar ya tabbatar da kotun cewa, tun bayan fitar waccan bidiyon har kawo zuwa wannan lokacin mai karar Adamu Abdullahi Karkasara baya iya yin bacci, sakamakon abunda ya faru na bata sunan mahaifin nasa.

Sai dai kuma daga bisani lauyan Sadiya Dauda Ican kabari, Barista Usaini Maqari, yayi roko a gaban kotun data basu wata ranar domin fara tattauna silhu duba da cewa akwai alaƙar harkoki siyasa tsakanin mai kara Adamu Abdullahi Karkasara da kuma Sadiya Dauda Ican kabari.

Lauyan mai kara Barista Tanimu Yahaya bai yi suka ba, kan akan rokon lauyan wacce ake karar na fara tattauna silhu domin ganin an fahimci juna.

Daga bisa Alkalin babbar kotun shari’ar musulinci dake Shahuci Malam Abdu Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa kotun ta amince da a fara tattauna silhu a tsakanin bangarorin guda biyu, ya kuma ce idan ba a samu sulhun ba za a ci gaba da gudunar da shari’ar tuhumar da ake yiwa Sadiya Dauda Ican kabari na bata sunan mahaifin mai kara Adamu Abdullahi Karkasara.

Ya kuma dage sauraron shari’ar zuwa ranar 13 ga wannan watan da muke ciki domin dora wa daga inda aka tsaya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.