SADIYA DAUDA ICAN KABARI TA LASHE AMAN TA A GABAN KOTU BAYAN BATA SUNAN MAHAIFIN WANI DAN SIYASA A NAN KANO.

0

Daga Ibrahim Aminu Riminkebe.

Matashiyar ‘yar siyasar nan Sadiya Dauda Ican kabari ta lashe aman ta bayan bata sunan mahaifin dan siyarar nan Adamu Abdullahi Karkasara a kafafan sada zumunta.

A baya dai kotun ta bada umarnin like wa wacce ake zargin takardar sammaci a Kofar gidan da kuma tura mata sakon karta kwana domin ta bayyana a gaban kotun, sakamakon zargin ita Sadiya Dauda Ican kabari tana gujewa shari’a.

Lauyan wacce ake zargin Barista Usaini Maqari ya nemi kotu data basu wata ranar domin fara tattauna silhu tsakanin bangarorin guda biyu sakamakon akwai alaƙar harkoki siyasa tsakanin mai kara a waccan zaman kotun daya gabata.

A zaman kotun na yau alhamis, karkashin jagorancin mai shari’a Malam Abdu Abdullahi Waiya, lauyan mai karar mai Barista Tanimu Yahaya ya bayyana wa kotun cewa, an samu silhu tsakanin mai kara da kuma wacce akai karar biyo bayan tattauwar fahimtar juna da suka yi.

Barista Tanimu Yahaya yace ita Sadiya Dauda Ican kabari tayi wani sabon bidiyo na lashe aman ta na bata sunan mahaifin Adamu Abdullahi Karkasara.

Ya kuma kara da cewa, sakamakon hakan ne ya sanya aka samu dai dai to, kamar yadda kotun ta bada umarnin tun a baya.

Wacce akai karar Sadiya Dauda Ican Kabari, bayan da kotun ta kalli sabon bidiyon data yi na bada hakuri ga mai karar, ta nuna nadamar ta tare da tabbatar wa da kotun cewa da wannan ranar ba zata sake ba.

Ta Kuma sake baiwa mai kara Adamu Abdullahi Karkasara hakuri a gaban kotun, tare da sake da bashi hakurin a rubuce domin kotun ta ajiye dukkanin bayanan a matsayin sheda.

Alkalin kotun Malam Abdu Abdullahi Waiya ya amince da silhu tare da jan kunan Sadiya Dauda Ican kabari data ringa tabbatar da magana kafin ta yada ta musamman a kafafan sada zumunta.

Leave A Reply

Your email address will not be published.