Sagagi United Ta Lashe Gasar Cin Kofin Hon. Aliyu Tukur Sagagi

0

Kungiyar Kwallon kafa ta Sagagi United ta lashe gasar cin kofin dan takarar Kansila na Mazabar Tudun Wuzurci a karamar Hukumar Birnin Kano Hon. Aliyu Tukur Sagagi.

Wasan karshen ya gudana a ranar Lahadi a Filin wasa na Makarantar Firamare ta Kofar Naisa dake nan Kano, kuma wasan karshen ya samu halartar dubban mutane.

Sagagi United wadda ta fito daga karamar hukumar Birni, ta samu nasara ne da ci 1-0 a kan Gwangwazo United wadda itama daga wannan karamar hukuma ta ke.

Gasar an shirya ta ne tsakanin kungiyoyin da suka fito daga mazabar Tudun Wuzurci, a yunkurin samar da zumunci tsakanin mazauna yankin da ma Kano baki daya.

Haka zalika gasar wadda ke zama irinta farko da Hon. Aliyu Sagagi ya shirya, ta samu tagomashi na halartar manyan bakin da suka halarci wasan karshen.

Masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Birnin Kano sun halarci wasan karshen, cikin su har da Shugaban ma’aikatan fadar Gwamnan Kano Shehu Wada Sagagi da ya samu wakilcin hadiminsa namusamman.

Hon Aliyu Tukur Sagagi wanda shi ne Dan Takarar Kansali a Mazabar Tudun Wuzurci, ya bayyana dalin shirya gasar dama fatansa ga Matasan wannan Mazaba.

Sagagi ya ce sun shirya gasar ne domin kawo sauyi a rayuwar matasa da suke dabi’ar shaye-shaye, wanda shirya gasar zai sanya suji suma ana damawa da su.

Ya kuma ce sun cimma nasarori da dama bayan shirya wannan gasar, musamman hadin kai da kuma goyan baya da suka samu na mazauna yankin.

”Muna jinjina ga wadanda suka halarci wannan gasa da muka shirya, muna shirin sake shirya wata gasar a gaba, kuma du ka Mazabun Karamar hukumar Birnin Kano zasu fafata,” a cewar Hon Aliyu.

Ya kuma godewa duka wadanda suka taimaka gasar ta gudana tsakanin matasan yankin, har ma ya ce wannan damba ce da suka sanya a gaba ta bawa matasa gudun mawa da suke fatan yi a ko yaushe.

Leave A Reply

Your email address will not be published.