Barau FC ta Raba Kayan Wasanni ga yan Wasan Makarantar Masu Bukata Ta Musamman Dake Tudun Maliki

0

Kungiyar kwallon kafa ta Barau FC, ta raba kayan wasannin kwallon kafa ga yan wasan Masu Bukata Ta Musamman da ke Tudun Maliki a nan jihar Kano.

Cikin Wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar Ahmad Hamisu Gwale ya fitar ya bayyana taron mika kayan wasannin ga yan wasan ya guda a ranar Litinin a harabar Makarantar da ke unguwar Tudun Maliki a karamar hukumar Kumbotso.

Da yake mika kayan wasannin da suka hada da riguna sawa da kwallo, da kuma rigunan daukar horo shugaban kungiyar ta Barau FC Alhaji Ibrahim Shitu Chanji ya ce sun bayar da kayan ne domin suma yan wasan su ji ana damawa da su.

Ibrahim Chanji, ya kara da cewa kungiyar ta Barau FC za ta ci gaba da tallafawa irin wadannan makarantu a wani yunkuri na ganin an tallafi harkokin wasanni.

Ya kuma ce uban kungiyar Sanata Barau Jibrin a shirye yake wajen tallafawa masu bukata ta musamman a ko ina suke, musamman domin bunkasa harkokin wasanni.

A jawabinta Daraktar ayyukan ta makarantar da ke Tudun Maliki Hajiya Umma Musa Abubakar, ta yiwa Allah godiya da wannan abin alkhairin da suka samu.

Ta kuma yi fatan samun nasara a dukannin al’amuran kungiyar ta Barau FC a kowanne irin mataki, tana mai cewa ko da yaushe za su ci gaba da yiwa Barau fatan samun nasara.

Ibrahim Chanji ya samu rakiyar ma’aikatan kungiyar ta Barau FC da suka hadar da Yahya Muhd, Ismail Mahmuda, Umar Lawan Yusuf.

Sauran sune Jabir Hassan, Abubakar Sadiq, Surajo Mukhatar, Aliyu Lawan, Sani Idris, Aminu Muhd Lash, Bilyaminu Umar and Ashiru Sheka.

Leave A Reply

Your email address will not be published.