Tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan Sheikh Abubakar Giro Argungu sakamakon rasuwarsa bayan gajeriyar jinya a ranar Laraba.
Independent Mirror ta rawaito cewa a Ranar Alhamis ne da aka gudanar da jana’izar marigayi Sheikh Giro wanda al’umma da dama suka halarta.
“Ina miƙa ta’aziyyata ga iyalai da mabiyansa,” a cewar Buhari.
Shugaba Buhari ya kuma ce yana mai addu’ar “Allah ya ji ƙan sa, ya saka shi cikin Jannatul-Firdaus”.
“Matuka ya tsaya kan ɗabi’un Musulunci tare da nuna jajircewarsa a aikace wajen gyara tarbiyyar al’umma ta hanyar wa’azinsa da ayyukansa.”
A ranar Alhamis aka yi jana’izar malamin a masallacin Idi na garin Argungu da ke jihar Kebbi, inda dubban mabiyansa suka halarci binne shi.
BBC