Da yiwuwar a ci gaba da samun ruwan sama mai karfi a birnin Makka-Rahoto

0

Rahotanni daga kasar Saudiyya na cewa akwai yiwuwar za a ci gaba da samun ruwan sama da tsawa a mafi yawan sassan ƙasar Saudiyya har zuwa ranar Juma’a mai zuwa.

Independent Mirror ta rawaito Jaridar Saudi Gazette ta ce bisa hasashen yanayin daga sassa daban-daban na Masarautar Saudiyya, Hukumar tsaron fararen hula na kira ga al’umma da mazaunan ƙasar su ɗauki matakan riga-kafin da suka wajaba, don tabbatar da ganin ana aiki sau da ƙafa da umarni da kuma gargaɗin da aka bayar.

Abu ne da ya wajaba ga kowanne mutane su kasance a wurare masu aminci a lokacin irin wannan tsawa kuma su kauce wa ƙoramu da fadamu da kurmi da sauran wuraren da ruwa ke da yiwuwar taruwa, sannan hukumar kula da tsaron fararen hula ta gargaɗi mutane su guji ninƙaya a wurare marasa aminci.

Hukumar tsaron fararen hula ta nuna cewa sassan biranen Makkah da Asir da Jazan da Al-Baha za su fuskanci ruwan sama matsakaici ko kuma mamako da ka iya janyo ambaliyar ruwa, wanda iska zai iya zuwa da iskar da ke iya tayar da ƙura.

A yankin Makkah, ana sa ran samun ruwan sama a Taif da Al Jumum da Bahrah da Al Qunfudhah da Al-Lith da Al-Kamil da Khulais da Maysaan da Adham da kuma Al-Ardhiyat kamar yadda BBC ta wallafa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.