Kungiyar kwallon kafa ta Turbo Touch Football Club, ta lashe gasar kwamandan rundunar sojin Najeriya, na bataliya ta 73 dake barikin Janguja da ke nan jihar Kano.
Wasan karshe na gasar da aka yiwa take da gasar Commanders Unity Cup 2025, da bataliya ta 73 ta shirya, an fafata a filin wasa na Janguza da ke nan Kano.
Turbo Touch FC, ta lashe gasar ne bayan nasara kan nasara a kan J. Shining Star FC da ci 2-1 a wasan karshen da suka fafata a ranar Lahadi, kuma ya samu halartar manyan baki.
Jim kadan bayan tashi daga wasan a zantawarsa da manema labarai, Birgediya Janar Ahmad Muhammad Tukur, ya ce gasar ta kayatar, kuma an shirya tane domin wanzarda zaman lafiya tsakanin kungiyoyi da al’umma.
Ya kara da cewa akwai shirin ci gaba da shirya irin gasar a nan gaba, domin hada kan matasa musamman domin bunkasa harkokin wasanni.
Ya kuma godewa wadanda suka halarci wasan karshe na gasar, musamman hadin kan da suka bayar wanda aka samu nasara kan gasar.
Haka zalika wasan karshen ya samu halartar manyan baki ciki har da babban Kwamanda a rundanar wato MAJ H. Idris FSS, Dr. Rabiu Sharif Inuwa Ahlan, Shugaban Hukumar kwallon Kafa ta Jihar Kano da sauran manyan baki.
Rundunar Soji ta kuma bukaci al’umma da su ci gaba da kasancewa masu son zaman lafiya, musamman kokarin hada kan al’umma da shirya irin wannan wasa na kwallon kafa.



