Ahmad Hamisu Gwale
Kungiyar Kwallon Kafa Ta Barau FC dake a matsayin gasar cin kofin kwallon kafa na Najeriya (NNL) ta samu maki a ranar Lahadi a kan kungiyar kwallon kafa ta Zamfara United, a wasan da suka fafata a filin wasan kungiyar ke amfani da shi a Birnin Kebbin jihar Kebbi.
Dan wasa Osondu Jonathan ne ya ci kwallo ta farko a minti na 50 da fara wasa, mintuna kadan da dawowa hutun rabin lokaci, bayan da Murtala Ibrahim ya taimaka masa.
Sai dai kungiyar Zamfara United ta warware kwallon a minti na 81 mintuna kafin kammala wasan.
Mai tsaron ragar kungiyar Barau FC Salim Ali, ya yi abun azo a yaba a wasan, inda ya hana kwallaye masu kyau shiga raga a wasan da aka shafe mintuna 90 kuma aka tashi 1-1.
Da wannan maki da kungiyar ta samu a waje, kunguyar ta Maliya na ci gaba da fatan dawowa zagaye na biyu na NNL da kwarin gwaiwa.
A zantawarsa da manema labarai bayan kammala wasan, jagoran kungiyar Barau FC Rabi’u Tata, ya bayyana gamsuwa da kokarin ‘yan wasansa.
Ya ba da tabbacin cewa kungiyar za ta sake dawowa a zagaye na biyu na gasar da kwarin gwiwa.
Kungiyar Barau FC ta koma matsayi na biyar da maki 6 a wasanni shida a teburin gasar NNL ta kakar 2024/2025.
Yanzu haka tawagar Maliya za su karbi bakuncin Zamfara United a ranar 15 ga watan Fabrairu, 2025, a filin wasa na Dambatta, jihar Kano.