Ahmad Hamisu Gwale
Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabiru Yusuf, ya cika alkawarin biyan sama da naira Miliyan 11 ga iyalan Marigayi Alhaji Salisu Yaro, tsohon jami’in walwala na kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars ( Sai Masu Gida).
Gwamna Abba Kabiru ya bayar da chakin kudin ne ga iyalan Marigayi Yaro, ta hannun kwamishinan matasa da wasanni na Kano Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso.
Mustapha Kwankwaso, wanda ya ziyarci gidan Marigayi Salisu Yaro a ranar Juma’a, ya mika chakin kudin ga iyalan Marigayin domin suyi amfani da kudin wajen kula da rayuwarsu.
A baya dai Alhaji Salisu Yaro, ya kasance babban jami’i a kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars, wadda ya hidimtawa shawon shekaru kafin ya rasu a farkon shekarar da muke ciki.
To sai dai Gwamnatin Kano karkashin gwamna Abba Kabiru Yusuf, ya ga dacewar biyan hakkokin da Marigayi Yaro yake bi a kungiyar ta Kano Pillars.
Lamarin da ya sanya a ranar Juma’a, kwamishinan matasa da wasanni na Kano Mustapha Rabiu Kwankwaso ya ziyarci gidan Marigayin tare da mika chakin kudin ga iyalan nasa.
Haka zalika Mustapha Kwankwaso ya kara da cewa, a baya ma sun biya wasu da dama hakkokinsu cikin wadanda suka hidimtawa kungiyar ta Kano Pillars.
Ya kuma ce, da sannu sauran wadanda suka hidimtawa kungiyar ta Kano Pillars, Gwamna Abba Kabiru Yusuf zai biya su hakkokinsu da suke bi.