Sanatan Borno ta Kudu Muhammad Ali Ndume ya bayyana ko za a kashe shi ba zai daina fadawa shugabanni gaskiya musamman halin kunchi da Al’ummar Najeriya ke fuskanta.
Independent mirror ta ruwaito cewa Sanata Ali Ndume ya ce: “Kowa ya san abin da ke faruwa a ƙasar nan. Kowa yana ji a jikinsa. Kuma ba laifi ba ne in gaya ma shugaban ƙasa don a kawo gyara”.
Ndume wanda kusa ne a jam’iyyar APC mai mulkin kasa ya ce zai ci gaba da faɗa wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu gaskiya, ko da hakan zai janyo masa kora daga jam’iyyar.
Sai dai ga dukkan alamu, ko Shugaba Tinubu bai ga laifin waɗannan kalamai ba, to ran jam’iyyarsa ta APC ya ɓaci, abin da ya sanya ta fitar da sanarwa tana yi wa Sanata Ndume gargaɗi.
APC ta nunar cewa Ali Ndume, babban ɗan jam’iyya ne kuma sanata sannan yana da ƙima sosai a idonta da kuma jama’a, don haka in ji ta, bai kamata duk lokacin da za a ambace shi, sai a ce ya yi wani abu da zai tozarta jam’iyya ba.
Ta ce an ambato sanatan a baya-bayan nan yana iƙirarin cewa Shugaba Bola Tinubu yana zagaye da mashawarta waɗanda ba nagari ba, ko kuma ƴan hana ruwa gudu da ke toshe hanyar da za a je, a ba shi shawara tagari.
A watan Yulin da ya wuce ma, sai da jam’iyyar APC ta nemi Majalisar Dattijai ta tuɓe Sanata Ndume daga muƙaminsa na mai tsawatarwa a majalisar saboda zargin sukar gwamnatin Shugaba Tinubu.
Daga bisani dai sanatan ya nemi afuwa, amma har yanzu ba a mayar da shi kan muƙamin mai tsawatarwar ba.
Sanata Ndume ya ce yana magana ne a bainar jama’a saboda ba ya samun damar ganin shugaban ƙasar, balle ya je ya faɗa masa halin da al’ummar Najeriya ke ciki kamar yadda ya shaidawa BBC.
Acewarsa, haƙƙi ne a kansa, ya ba da shawara a matsayinsa na dattijo.
APC dai ta ce babba mai ƙima kamar Ali Ndume, bai kamata a ce ana yamaɗiɗi da sunansa a matsayin wanda ke ƙoƙarin tozarta martabar jam’iyya ba.
Amma Ndume ya ce a duk bayanansa babu inda ya aibata wani, kuma babu inda ya soki jam’iyya ko shugaban ƙasa.
Ya ce duk maganar da ake yi matuƙar dai game da shawara ce, to yana nan a kan matsayinsa.
Sanatan ya ce ya bi duk hanyar da zai iya bi don ganin ya samu damar ganin shugaban ƙasar saboda ya bayyana masa halin da ƴan Najeriya ke ciki amma bai yi nasara ba.
Ya ce yana magana ne domin sauke nauyin al’umma da ke kansa a matsayinsa na mai wakiltar jama’a