An yabawa jam’iyyar PDP a jihar Kwara bisa rabon takin zamani da jam’iyyar ta yi a yankin Kwara ta Arewa domin tallafawa manoma kuma ƴan jam’iyya.
Shugaban jam’iyyar na Kwara ta Arewa, Hon. Ndako Pkada ne yayi wannan yabo a wata sanarwa da ya fitar a ranar juma’a inda ya ce taimakon takin zamanin zai taimaka sosai ga ƴan Jam’iyyar musamman a wannan yanayi na damuna.
Shugaban ya ƙara da cewa rabon takin zamanin ya nuna yadda jam’iyyar PDP a jihar Kwara ta damu da ƴan jam’iyya.
Sannan kuma ya yabawa shugaban jam’iyyar na jiha, Alhaji Tunde Muhammad bisa irin jagorancinsa da yadda yayi ƙoƙarin ganin takin ya kai ga manoman saboda suna matuƙar buƙatarsa.
Sannan ya yabawa Dr. Abubakar Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa ta ƙasa, bisa yadda ya zama cikakken jagora sannan da kasancewarsa mutum jajirtacce.
Ya ce “Tabbas shugabancin jam’iyya ya nuna irin damuwar da yayi ga ƴan Jam’iyya kuma za mu ci gaba da jajircewa wajen ganin jam’iyyar ta samu nasara duk da cewa ba mu ne muke da gwamnati ba a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya ba”
Shugaban jam’iyyar ya yi kira ga waɗanda suka ci gajiyar shirin cewa su yi amfani da takin zamanin wajen yin noman a yayin da ake ci gaba da fuskantar matsalar abinci a fadin Nigeria baki ɗaya.