Wani Matashi mai suna Ubaidullahi Saleh wanda a Kafi sani da Ubaidu Tilde ya gudanar da tattaki daga jihar Bauchi zuwa Kano biyo bayan nasarar Gwamna Abba Kabiru Yusuf a Kotun Koli.
Ubaidullahi mai shekara 30 a duniya, wanda dan asalin garin Tilden Fulani ne dake karamar Hukumar Toro a jihar Bauchi, ya yi Tattakin ne kafa da kafa tun daga garin Tilde har zuwa garin Kano domin taya gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf samun Nasara a kotun koli.
Ubaidu Tilde ya bayyana cewa “nayi wannan Tattaki ne, ba dan komai ba sai dan Kauna da soyayyar da nake yiwa gwamna Abba Kabiru Yusuf, kuma na yiwa Kaina Alkawari zanyi wannan tafiya domin taya Abba gida gida murna.”
Matashi Ubaidullahi Saleh ya kuma kara da cewa takkakin na zuwa ne bayan da suma kanawa suka yi cincirindo domin tarbar Gwamna Abba Kabiru Yusuf.
A ranar Lahadi ne Gwamnan Kano Abba Kabiru Yusuf ya tawo daga jihar Kaduna zuwa Kano domin gaisawa da Al’ummar jihar Kano wanda suka fito domin nuna soyayyarsu gare shi.
Idan za a iya tunawa a ranar Juma’ar data gabata 12 ga watan Junairu shekarar 2024, Kotun Kolin kasar nan ta tabbatar da Abba kabir Yusuf a matsayin hastaccen Gwamnan jihar Kano.