Tsohon dan takarar Gwamnan Kano a zaben 2023 Dr Nasiru Yusuf Gawuna ya biyawa daliban Jami’ar Bayero Mata Yan Asalin Kano su kimanin 100 kudin Makaranta.
Independent Mirror ta rawaito cewa Gawuna wanda Tsohon Mataimakin Gwmanan Kano ne ya biya kudin na Dalibai Mata wanda suke Shekarar karshe a Jami’ar ta Bayero su kimanin 100.
Jumullar kudin da Gawuna ya biyawa daliban kudin Makaranta ya kai sama da Miliyan Goma Sha daya.
“Tuni Jami’ar Bayero ta Mika sunayen Dalibai Mata 100 ga Nasir Gawuna, daliban wanda suke Shekarar karshe a Jami’a kuma sune wanda suka gaza biyan kudin Makaranta” A cewar guda cikin Malaman Jami’ar.
Haka zalika Jami’ar ta Bayero ta karbi shaidar biyan kudin da Nasir Gawuna ya biyawa daliban Jami’ar kudin na Karatu da suka gaza biya.
Guda cikin Malaman Jami’ar ta Bayero ya ce tuni Nasir Gawuna ya aiko da shedar biyan kudi ta kimanin Naira Miliyan 600,0000 da karin Naira Miliyan 5 da dari 8 da kuma Dubu 27,000.
Idan za a iya tunawa dai Gwamnatin Kano ma tayi Alkawarin biyawa daliban Jami’ar ta Bayero kudin Makaranta, wanda har kawo yanzu ake jiran dakon biyan kudin ko dai daga bangaren Gwamnatin ko kuma bangaren Jami’ar ta Bayero kamar yadda Jaridar Politics Digest ta buga Labarin.