An Zargi Mali da Tursa sa Matasa don yin Zanga-Zanga

0

Daga Mustapha Muhammad Kankarofi 

Ana zargin kasar Mali da tursa sa Matasan kasarta don yin Zanga-zanga Domin nuna Goyon Bayansu game da Ficewarta Daga Kungiyar ECOWAS.

Gwamnatin Mali na shirin tilastawa matasan kasar ta Mali domin goyon bayan ficewarta daga kungiyar ECOWAS.

Sai dai wasu bayanai da manema labarai suka samu daga wata wasika da da ake zargin ta nuna cewa gwamnatin Mali ta sanya jami’anta na tilastawa ‘yan kasar ta goyon bayan Mali kan ficewar da tayi daga ECOWAS.

Haka zalika cikin bayan da manema labarai suka samu a kasar ta Mali a cikin wata wasika tana cewa “Gwamnatin Mali, ta hannun Ministan Matasa da Wasanni, ta yi kira ga jama’a da su hada kai don goyon bayan shawarar janyewar kasar daga kungiyar ECOWAS daga Burkina Faso, Mali, da Nijar da suka yi.

Idan dai za a iya tunawa, Mali da Burkina Faso da Nijar sun sanar da cewa, sun aikewa da kungiyar ECOWAS, sanarwar ficewarsu daga kungiyar.

Hukumomin sojan kasashen uku sun sanar da shirin ficewa daga kungiyar ta yammacin Afirka, bisa zarginsu da yin barazana ga ikonsu wanda ya sanya kugiyar ta ECOWAS ta nuna tashin jin dadin ta ficewar kasashen daga kungiyar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.