A karo na biyu NNPP ta sake rasa kujerar majalisar tarayya a Kano

0

Kotun sauraren kararrakin zaben yan majalisar tarayya dana jiha da ke zamanta a Kano, ta ayyana Musa Ilyasu Kwankwaso na jami’iyyar APC a matsayin sabon dan majalisar yankin Kura- Madobi da Garun Malam.

Independent Mirror ta rawaito cewa kotun ta soke nasarar da INEC ta bawa Umar Datti Kura na jam’iyyar NNPP nasara bisa rashin bai ajje aiki ba kwanaki 30 kafin zaɓen Dan majalisar wakilai na yankin .

Mai shari’a Flora Ngozi Azinge ce ta tabbatar da hakan cikin wani hukunci da ta yanke a ƙarar da Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso da ya yiwa jam’iyyar APC takarar kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltar Kura- Madobi da Garun Malam.

Kotun ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta janye Shaidar cin zabe da ta bawa Yusuf Umar Datti tun a baya, ta kuma ayyana Musa Iliyasu Kwankwaso a matsayin wanda ya lashe zaben kuma halastaccen dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kura Madobi da Garun Malam saboda shi ne yazo na biyu a zaben da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabarairu 202.

Ko a makon da ya gabata ma sai da kutun sauraren kararrakin zabe a Kano ta soke nasarar Mukhtar Yarima, na jami’iyyar NNPP sakamakon gabatar da takardun makaranta na bogi.

Mukhtar Yarima wanda Hukumar INEC ta ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben majalisar tarayya a karamar Hukumar Tarauni a zaben da ya gudana a ranar 25 ga Fabrairu.

To amma tuni kutun a zaman da ta gudanar a watan da ya gabata ta ayyana Hafizu Kawu na APC a matsayin sabon dan majalisar karamar Hukumar Tarauni.

Kawo yanzu NNPP ta rasa kujerun yan majalisar tarayya a yankin karamar Hukumar Tarauni da kuma yankin Kura-Madobi da Garun Malam.

Leave A Reply

Your email address will not be published.