Sanatan Kano ta Kudu Abdulrahman Kawu Sumaila ya ziyarci garin da gadar Kogin nan ta karye a Kayadda da Fajewa a karamar hukumar Takai a ranar Alhamis.
Independent Mirror ta rawaito cewa Sanatan ya samu rakiyar kwamishinan sufuri na Kano Muhammad Diggol da sauran rakiyar wasu magoya bayansa.
Sanata Kawu Sumaila ya yi alkawarin kai musu daukin gaggawa tare da sake gina gadar da ta karye a Kauyen.
Wannan dai na zuwa ne biyo bayan rahoton wakilin Premier Radio 102.7 FM Aminu Abdullahi Ibrahim ya yi na karyewar gadar a makon da ya gabata.
Idan za a iya tunawa a Larabar data gabata ne muka kawo muku rahoton yadda karti Maza ke daukar Mata a kafada don tsallar dasu ruwan Kogi a karamar hukumar Takai sakamakon karyewar gada.

Ga wasu cikin Hotunan ziyarar ta Sanata Kawu Sumaila zuwa Kauyen na Kayadada a karamar Hukumar Takai.



