Tsohon shugaban majalisar dattawan kasar nan, Alhaji Abubakar Bukola Saraki Saraki ya kai ziyarar gani da ido, domin ganin yadda ake tantance ɗalibai 100 da gidauniyarsa ta Abubakar Bukola Saraki Foundation ta ɗauki nauyin karatunsu a jami’ar Muhammad Kamaldeen dake jihar Kwara.
A ziyarar tasa, Saraki ya jinjinawa kwamitin tantancewar bisa sadaukar da kai da suka yi da kuma yin aiki da gaskiya wajen tantance ɗaliban da kuma tabbatar da ganin kowanne a cikin su ya bi ƙa’idar da aka saka.
Kawo yanzu dai an kammala tantance ɗalibai 80 saura guda 20 inda tuni shirye-shirye suka yi nisa wajen fara karatun ɗaliban.
“Ilimi shi ne babban abin da na ɗauka da muhimmancin gaske saboda yana kawo ci gaba kai tsaye. Hakan ne ma yasa na mayar da hankali a kansa, kuma na kawo tsare-tsare a lokacin da nake cikin gwamnati da yanzu da yake ɗan ƙasa mai zaman kansa.” A cewar Saraki.
Sannan Saraki ya shawarci ɗaliban da basu cike ba suje su shiga shafin na yanar gizo https://t.co/Sf4y68SFrt domin su cike don a kammala gurbin mutum 20 da ba a samu ba tunda mutum 100 da aka yi niyyar ɗaukar nauyin karatun nasu.
A kwanakin baya ne dai Dr. Abubakar Bukola Saraki ya bayyana cewa zai ɗauki nauyin karatun ɗaliban 100 a jami’ar Muhammad Kamaldeen dake Ilorin ɗin jihar Kwara a ƙoƙarin sa na ci gaba da tallafawa harkokin ilimi a jihar Kwara da ma ƙasa baki ɗaya.