A shirye muke don  ci gaba da faɗakarwa kan muhimmancin ilimin Mata a karkara-kungiyar ODPMNigeria 

0

Kungiyar nan ta ODPM mai rajin kawo sauyi ga ci gaban al’umma da kuma siyasa ta ce babban abinda zata saka a gaba a sabuwar shekarar 2024 shine nusarwa kan muhimmancin ilimin mata musamman a yankunan karkara.

Shugaban kungiyar na kasa Amb. Umar Bello Galadima ne ya bayyana hakan yayin babban taron shekara da kungiyar ta gudanar a bana.

Taron kungiyar na bana ya ta’allaƙa ne akan nasarori da ƙalubalen da ƙungiyar ta fuskanta a shekarar da ta gabata.

Kafin fara taron dai an fara da muhawara da tattaunawa kan matsalar ƙarin kuɗin makarantun gaba da Sakandire da aka samu a Najeriya tare da kawo hanyoyin da ka iya kawo sauƙi ga ɗalibai.

A yayin taron, ƙungiyar ODPMNigeria ta lashin taƙobin aiwatar da wasu manyan ayyuka a wannan shekarar da suka haɗa da;
Dawo da shirin tallafawa marayu na ‘Hands to Orphans’ da ma makamantansu,Gabatar da shirin horarwa ga matasa akan sana’o’in zamani.

Kamar ko da yaushe taron ya samu jagorancin shugaban ƙungiyar na ƙasa Amb. Umar Bello Galadima da mataimakiyar sa Ummulkhairi Abubakar Ungogo da magatakardar ƙungiyar Mallam Zahraddeen Kabir da ma wasu daga cikin shuwagabannin ƙungiyar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.