Ƙungiyar ci gaban matasa ta ODPMNigeria ta gabatar da taron tattaunawa ta musamman da matasa a ƙaramar hukumar Bichi da nufin ci gaba da lalubu matsalolin al’umma.
Ƙungiyar ta samu haɗin gwiwar Ƙungiyar Majalisar Matasa ta Ƙasa reshen ƙaramar hukumar Bichi (NYCN) domin gabatar da wannan muhimmin taro.
A yayin taron, an tattauna akan matsalolin tsaro da ya ta’azzara a jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya tare da zaƙulo hanyoyin da ƙungiyoyi irin namu na matasa zasu bada gudunmawa wajen kawo ƙarshen matsalar a jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.
ODPMNigeria ta jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyoyin matasa da hukumomin tsaro, tare da kira ga matasa su kasance masu bayar da shawara da kuma taka rawar gani wajen samar da mafita maimakon su zama cikin masu haifar da matsalar.
An kuma yaba da irin goyon bayan da Ƙungiyar Majalisar Matasa ta Ƙasa (NYCN) reshen Bichi ta bayar, wanda ya tabbatar da nasarar taron.
Masu halarta sun bayyana gamsuwarsu tare da sha’awar ganin irin waɗannan tarurruka suna ci gaba da gudana a sauran yankuna na jihar Kano.
Taron ya ƙare da kira ga kowane matashi da ya kasance jakadan zaman lafiya, tare da yin aiki kafada da kafada domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a Kano da Nijeriya gaba ɗaya.