Gwamnatin tarayya ta kaddamar da aikin samar da wutar lantarki ta hasken rana mai karfin 7 megawatt a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), kasa da awa 48 bayan rikicin wuta tsakanin asibitin da kamfanin rarraba wutar Kano (KEDCO).
Shugaban kwamitin kasafin kudi na Majalisar Wakilai, Hon. Abubakar Kabir Bichi, wanda ke wakiltar mazabar Bichi, shi ne ya kawo aikin da darajarsa ta kai sama da naira biliyan 12.
Ya ce wannan bangare ne na shirin Renewed Hope na Shugaba Bola Tinubu na samar wa dukkan manyan makarantu da asibitocin koyarwa wutar hasken rana a fadin kasar.
Bichi ya bayyana cewa asibitin AKTH kadai ya samu ayyukan da kudinsu ya kai sama da naira biliyan 26 a bana, tare da shirin saka irin wannan tsarin a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), ADUSTECH Wudil, da asibitocin Murtala da Nasarawa.
Daraktan Hukumar Kula da Makamashi ta Kasa (ECN), Dr. Mustapha Abdullahi, ya tabbatar da cewa aikin zai kammalu kafin ƙarshen shekarar 2025, yana mai cewa wannan shi ne na farko a irin sa a Najeriya.
Ministan Kimiyya, Fasaha da Kirkire-Kirkire, Uche Nnaji, ya jinjina wa aikin bisa muhimmancin sa wajen aiwatar da shirin Renewed Hope.
Shugaban Asibitin AKTH, Farfesa Abdulrahman Sheshe, ya bayyana cewa asibitin na kashe sama da naira miliyan 180 duk wata wajen biyan wutar lantarki da dizal, yana mai cewa aikin zai rage kudaden kashewa da kashi 30 cikin 100 tare da tabbatar da ci gaba da samun wuta ba tare da yankewa ba.