Gwamnan Kano Abba Kabir ya ce ko kaɗan hukuncin ba zai rage musu ƙwarin gwiwa ko ya sanyaya musu gwiwa ba a kan yadda suke gudanar da ayyuka ga al’ummar jihar ta Kano ba.
Independent Mirror ta rawaito cewa gwamnan ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa suna fatan kotun ɗaukaka ƙara ta kasar nan za ta gyara kura-kuran da ya ce wannan kotun ta farko ta yi wajen soke nasarar tasa.
Gwamnan ya bai wa al’ummar da suka zaɓe shi tabbacin cewa kotun ɗaukaka ƙara wadda suke da damar garzayawa gare ta a nan gaba za ta tabbatar masa ikon da jama’a suka ba shi na mulkinsu.
Ya jaddada cewa hukuncin ba zai sa su ja da baya ba za su tsaya tsayin daka bakin ƙarfinsu domin ganin nasarar da suka samu a zaɓen ta tabbata a wannan lokaci.
Gwamman ya kuma lashi takobin cewa idan har ita ma kotun ɗaukaka ƙara ba ta yi musu hukuncin da ya gamsar da su ba, za su yi amfani da damar da suke da ita wajen garzayawa har zuwa kotun ƙoli.
A yayin jawabin da ya gabatar ya kuma roƙi al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata matsala ko tashin hankali ba.
Ita dai kotun da ta yi hukuncin wadda ta kasance ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Flora Ngozi Azinge ta soke nasarar Abba Kabir Yusuf ne bayan ta shafe wajen wata shida na sauraren bahasin kowane ɓangare a shari’ar.
Bayan sanar da matsayar kotun sauraron korafin zaben gwamnan a ranar Laraba, hukumomin jihar sun kakaba dokar hana fita domin gudun kauce wa tashin hankali.
Ko a lokacin da Hukumar zaben Najeriya ta sanar da nasarar Abba Kabir a zaben da ya gudana a watan Maris, an samu asarar dukiya a birnin na Kano, sanadiyyar murna daga wasu magoya baya.