Rahotanni sun bayyana kawo yanzu haka Tawagar yan Jaridun Najeriya 20 ta isa kasar Africa Ta Kudu, a wani bangare na ci gaba da karbar horo da suke kan aikin jarida na zamani.
Independent Mirror ta rawaito cewa
Daga cikin yan jaridun 20 din harda ma’aikacin Premier radio, Abdulrasheed Hussain, wadanda aka zaba bayan rubuta jarabawa tsakanin yan jaridu kusan dubu uku da suka fafata wajen nema.
Horan na tsawon watanni 6 an fara shi ne tin a watan Mayu, a jami’ar Pan Atlantic da ke jihar Lagos wanda kuma a yanzu suka tafi kasar Africa ta Kudu domin ci gaba da daukar horon, in da za su shafe kwanaki 10 a can.
Abdurrashid Hussain wanda Editane a tashar Premier Radio 102.7 Kano ya samu wannan nasara ne daga cikin takwarorinsa.
Hussain ya Kammala karatunsa na Digiri a Jami’ar Bayero da ke nan Kano a bangaren aikin Jarida.
Kuma yanzu haka yana daga cikin manyan maaikatan Premier Radio da suka fara aiki a kafar kasa da shekara biyu da bude ta.
Ya kuma yi aiki a baya da kafafen Labarai a Kano irinsu Aminchi da kuma Nasara Radio.
Kamfanin MTN ne dai ya dauki nauyin dukkan bayar da horon, karkashin wani shiri da ya bullo da shi domin karfafa aikin yan jaridu da kafafan yada labarai.