Abin da ya sa muka Kori kwamishinan kasa da Ogan Boye-Gwamnatin Kano

0

Gwamnatin  jihar Kano ta bayyana ta Sallami kwamishinan ma’aikatar kasa da safayo na Kano Adamu Kibiya da mai baiwa gwamna Shawara kan harkokin Matasa da wasanni Amb. Yusuf Imam bisa kalaman tunziri.

Independent Mirror ta rawaito a wani Taron manema Labarai na gaggawa da Kwamishinan yada labarai na Kano Baba Halilu Dantiye ya jagoranta a daren juma’ar nan an jiyo gwamnatin ta dauki wannan matakin.

A ranar Alhamis a wajen Taron addu’o’in da yan jam’iyyar NNPP suka gudanar a Kano, aka jiyo kwamishinan da Oga Boye suna kalaman tunzura al’umma kan Shari’ar zaɓen gwamnan Kano da ake dakon hukunci daga kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan kano.

Tuni ma dai wannan batu ya ke ci gaba da daukar hankali jama’a bisa kalaman da aka jiyo masu ruke da madafun iko a Gwamnatin sunyi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.