Tsohon Mataimaki namusamman ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan kafofin sada zumunta wato Abubakar Aminu Ibrahim, ya fitar da shaidar biyan Kudin daliban Jami’ar Bayero Mata 100 da Nasir Yusuf Gawuna ya yi.
Independent Mirror ta rawaito cewa, wannan na zuwa ne bayan da ake ta cece-kuce kan sahihancin biyan kudin Makarantar daliban da Gawuna ya ce ya yi.
A makon da ya gabata ne wata wata Jaridar Internet ta wallafa Nasir Yusuf Gawuna ya biyawa daliban Jami’ar Bayero Mata Yan ajin karshe kudin Makarantar har Sama da Miliyan 11.
To sai dai Abubakar Aminu Ibrahim wanda tsohon Mataimaki namusamman ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan kafofin sada zumunta ne ya wallafa shaidar biyan kudin da Gawuna ya yi.
Abubakar Aminu Ibrahim a shafinsa na Facebook ya wallafa cewa “Ga Shaidar (Receipt) biyan Kudin Registration Na Daliban BUK Daga Dr. Nasir Yusuf Gawuna.
“Ina na Kantoman Kano da yayi alkawari har yau ya kasa biya”
To amma Independent Mirror ta tuntubi Mai magana da yawun Jami’ar ta Bayero Lamara Garba Azare ya ce ba shida masaniya kan wannan batu.
A bangaren Gwamnatin Kano karshin Gwamna Abba Kabiru Yusuf ita ta sanar zata biyawa daliban Jami’ar Bayero kudn Makaranta.
Sai dai har kawo yanzu babu wata Sanarwa ta biyan kudin daga bangaren na gwamnatin Kano.